Rooney na so a daina Premier a kirsimeti

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rooney ya ce buga wasa a lokutan kirsimeti zai sa 'yan wasa su rika jin rauni

Kyaftin din Manchester United, Wayne Rooney, ya bukaci a canja tsarin buga gasar Premier domin a daina yi a lokacin bikin kirsimeti.

Rooney, mai shekaru 29, ya ce yawan buga wasannin a lokacin hutun kirsimeti yana rage karsashin gasar.

Dan wasan ya kara da cewa ‘yan kwallo suna gajiya matuka, kuma yin wasan a lokutan kirsimeti zai iya yin sanadiyyar jin rauni mai muni ga dan wasa.

A gasar Premier ana buga wasanni biyu daga tsakanin 26 zuwa 28 ga watan Disambar kowacce shekara.

Shi ma kocin United, Louis van Gaal, ya ce ‘yan wasansa sun sha dawainiya bayan da suka tashi babu ci tsakaninsu da Tottenham, kuma awanni 43 tsakani da suka buga wasa da Newcastle.