Gareth Bale ba zai bar Madrid ba - Perez

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bale ya zura kwallaye a gasar Champions League da kuma wasan karshe na cin kofin Copa del Rey.

Shugaban La Liga, Florentino Perez, ya ce dan wasan Real Madrid, Gareth Bale ba zai taba barin kulob din ba.

Bale, mai shekaru 25, ya koma Real daga Tottenham a kan kudi fam £85.3m a shekarar 2013, kuma ana ta yin rade radin cewa zai koma Manchester United.

Sai dai Perez ya shaidawa jaridar Marca ta kasar Spaniya cewa,"Ba mu samu wata bukata daga Manchester da ma duk wani kulob ba game da komawar Gareth Bale can."

Ya kara da cewa "Kamar dai yadda bana tsammanin Cristiano Ronaldo zai bar Real Madrid, haka ma bana tunanin cewa Bale zai bar Real."

Bale ya zura kwallaye a gasar Champions League da kuma wasan karshe na cin kofin Copa del Rey.