Gerrard zai bar Liverpool

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool na tangal-tangal a kakar wasa ta bana

Kyaftin din kungiyar Liverpool, Stephen Gerrard ya sanarda cewa zai bar kulob din a karshen kakar wasa ta bana.

Gerrard dan shekaru 34, ya shafe tsawon rasuwarsa yana taka leda a Liverpool tun bayan da ya hade da tawagar tun yanada shekaru takwas da haihuwa.

Ya bayyana matakinsa na barin kungiyar a matsayin matakin mafi wuya a rayuwarsa bayan ya buga wa Liverpool wasanni 695 inda ya zura kwallaye 180.

Ana saran Gerrard zai koma wata kungiya a Amurka.

Ya bayyana cewa ba zai iya buga wa wata kungiya da ke hammaya da Liverpool ba.

Shekaru goma da suka wuce, Gerrard ya jagoranci Liverpool ta lashe gasar zakarun Turai inda ta doke AC Milan a wasan karshe.