Ana tuhumar wani mutum da cin zarafin Wenger

Image caption Mutumin zai bayyana gaban kotu

Ana tuhumar wani mutum bisa zargin neman manajan Arsenal, Arsene Wenger da fada, a lokacin wasan kulob din da Southampton ranar farko ta sabuwar shekara.

Ana zargin Luke Bryant mai shekaru 25 da haihuwa wanda kuma ya fito daga Lymington, yankin Hamshire da karya dokar wasan kwallon kafa ta duniya ta 1991 saboda zuwa kusa da filin wasa da ya yi.

Wanda ake tuhumar zai bayyana a gaban kotun majistre da ke a Southampton ranar 22 ga Janairu.

Bryant dai ya tunkari manajan Arsenal din mai shekaru 65, kafin 'yan sandan da ke filin su yi awon gaba da shi.

Sai dai kungiyar wasan Southampton ta ce Bryant masoyin kulob din Arsenal ne amma Wenger ya yi imanin mutumin mai goyon bayan kungiyar Southampton ne.

Al'amarin dai ya biyo bayan cin mutumcin da magoya bayan kulob din na Arsenal su ka yi wa Wenger a lokacin da ya ke hawa jirgin kasa bayan rashin nasarar kulob din a Stoke a watan Disamba.