Arsenal ta fara kare kofinta na kalubale

Arsenal Hull Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A bara ma Arsenal ce ta doke Hull City ta kuma lashe kofin kalubalen

Arsenal ta fara kare kofinta na kalubale da kafar dama, bayan da ta doke Hull City da ci 2-0 a wasan da suka fafata ranar Lahadi.

Per Mertesacker ne ya fara zura kwallo daga bugun da Alexis Sanchez ya yo masa, kafin Sanchez din ya kara zura kwallo na biyu a raga.

Arsenal ce ta fi taka leda a mintina na 45 kafin a tafi hutu, kuma Hull ta yi kokarin ta rama kayen da ta sha a wasan karshe da suka kara a bara.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Dover 0 - 4 Crystal Palace QPR 0 - 3 Sheff Utd Sunderland 1 - 0 Leeds Aston Villa 1 - 0 Blackpool Man City 2 - 1 Sheff Wed Southampton 1 - 1 Ipswich Stoke 3 - 1 Wrexham Yeovil 0 - 2 Man Utd Chelsea 3 - 0 Watford