PSG ta hukunta Lazezzi da Cabani

Edison Cabani Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption PSG tace ba za ta yarda da halin rashin da'a ba dalilin da yasa ta hukunta 'yan kwallon 2

Kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain ta Faransa ta hukunta Ezequiel Lavezzi da Edinson Cavani saboda ba su dawo daga hutun da kulob din ya bayar da wuri ba.

Saboda haka 'yan wasan biyu ba za su buga wa kulob din wasanni biyu da zai buga nan gaba ba, sannan kuma za su biya tarar kudi.

PSG za ta kara da Montpellier a gasar kofin kalubale ranar Litinin, sannan ta fafata da Bastia ranar 10 ga watan Janairun bana.

'Yan wasan biyu ba su halarci wasan sada zumunta da kulob din ya kara da Inter Milan a Morocco ba, sannan ba su halarci filin atisaye a ranar sabuwar shekara ba.

Ana ta rade-radin Ezequil Lavezzi zai bar kulob din a watan Janairu zuwa wata kungiyar a Ingila.