'Na dade ina shirya yadda zan doke Barcelona'

Messi Moyes Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona ta barar da damar hayewa kan teburin La Liga

Kocin Real Sociedad, David Moyes, ya ce ya dade yana tunanin hanyoyin da zai bi ya doke Barcelona idan suka hadu a wasa.

Kocin ya fadi hakan ne bayan da suka tashi wasan La Liga na mako na 17, a inda suka doke Barcelona da ci daya mai ban haushi.

Jordi Alba ne ya zura kwallo a ragar Barcelona a minti na biyu da fara tamaula, kuma nasarar da suka samu ya sa sun koma mataki na 13 a teburin La Liga.

Manchester United ce ta kori Moyes wanda ya gaji Sir Alex Ferguson, bayan da ya jagoranci kulob din tsawaon watanni 10 kacal.