Ghana na jiran sakamakon raunin Schlupp

Jeff Schlupp Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ghana na fatan taka rawar ganai a gasar da Equatorial Guinea za ta karbi bakunci

Kasar Ghana na jiran sakamakon raunin da Jeff Schluff ya ji domin tantance idan zai iya buga mata gasar cin kofin Nahiyar Afirka na bana.

Ghana ta saka sunan Schlupp a cikin tawagar 'yan wasan da za su wakilce ta a gasar da za a fara daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun 2015.

Sai dai kocin Leicester City Nigel Pearson ya ce tabbatar da ko dan kwallon zai iya buga gasar kofin nahiyar Afirka ya dogara ne da sakamakon gwajin raunin da likitoci suka yi masa.

Ghana tana cikin rukuni na uku wanda ya kunshi Algeria da Senegal da kuma Afirka ta Kudu.