Mourinho ya yi nadama kan alkalin wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya ce Friend kwararren alkalin wasa ne.

Kociyan Chealsea, Jose Mourinho ya nemi afuwar alkalin wasa Kevin Friend bayan ya soke shi a kan rashin bai wa Chealsea bugun fenariti a lokacin da suka yi nasara kan Watford 3 -1 a ranar Lahadi.

Mourinho ya yi ikirarin cewa kin ba su bugun fenareti wani bangare ne na kokarin murkushe kulob din.

Amma daga baya ya canza kalamansa yana mai yabon Friend da kasancewa kwararren alkalin wasa.

Mourinho ya kara da cewa "ina mai nadamar kalaman da na yi a hira da wasu gidajen talabijin."

Friend dai ya shaida wa Mourinho cewa zai iya ba su bugun fenariti da dan wasan bai ci kwallon ba.