Shugaban Arsenal zai gina filin wasa a Amurka

Stan Kroenke Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana mataki na shida a teburin Premier da maki 33

Mutumin da ya fi yawan hannun jari a Arsenal, Stan Kroenke, na shirin sanya jarin gina katafaren filin wasan kwallon kafa a Los Angeles dake Amurka.

Los Angeles ne birni na biyu mafi girma a Amurka, amma ba shi da kulob din da yake buga gasar kwallon kafar kasar.

Kroenke ne ya mallaki kulob din Rams wanda aka kafa a Los Angeles, yanzu yana buga wasansa a St Louis tun daga shekarar 1994.

A cewarsa, yana shirin gina sabon filin wasa da zai iya daukar 'yan kallo 80,000 a Inglewood.

Stan shi ne mafi yawan hannun jari a Arsenal, inda yake da kaso sama da kashi 66 daga cikin dari a kulob din.