Gerrard zai koma Los Angeles Galaxy

Steven Gerrard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool za ta yi rashin Steven Gerrard wanda zuwa Los Angeles Galaxy

kyaftin din Liverpool, Steven Gerrard, na daf da kammala yarjejeniyar koma wa kulob din Los Angeles Galaxy ta Amurka a kwantiragin watanni 18.

Dan wasan, mai shekaru 34, zai rattaba kwantiragin da zai kai kudi fam miliyan shida, wanda zai zamo daya daga cikin 'yan wasan da suka fi daukar albashi a gasar.

Gerrard zai koma Galaxy a watan Yunin nan, lokacin da kwantiraginsa zai kare da Liverpool

David Beckham ya buga wa Galaxy wasanni tsawon shekaru biyar, kuma tsohon dan wasan Liverpool Robbie Keane yanzu yana yi wa kulob din wasa.