Atletico ta doke Real Madrid da ci 2-0

Atletico Real Madrid Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan ne karo na biyu da aka doke Real Madri a shekarar nan

Kulob din Atletico Madrid ya doke Real Madrid da ci 2-0 a gasar Copa del Rey da suka fafata a filin Vicente Calderon ranar Laraba.

Raul Garcia ne ya fara zura kwallo a bugun fenariti, kafin Gimenez de Vargas ya kara ta biyu saura minti 14 a tashi wasa.

Haka kuma Fernando Torres ya buga karawar a karon farko da ya koma kulob din wasa aro daga AC Milan na Italiya, sai dai an canja shi a wasan

Wannan ne karo na biyu da Madrid din ta sha kashi a shekarar nan, bayan da Valencia ta karya mata lagon lashe wasanni 22 da ta yi a jere.

A ranar 15 ga watan nan na Janairu Atletico za ta ziyarci Real Madrid a wasa na biyu da za su kara a filin Santiago Bernabéu.