Podolski ya fara buga wa Inter Milan tamaula

Lucas Podoski Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan ya koma taka leda Inter ne aro daga Arsenal

Lukas Podolski ya fara buga wa Inter Milan a karon farko a karawar da suka tashi kunnen doki da Juventus a ranar Talata.

Juventus ce ta fara zura kwallo a ragar Inter Milan, wacce Roberto Mancini yake horar wa ta hannun Carlos Tevez.

Podoslki, wanda ya koma Inter taka leda aro daga Arsenal, ya shiga wasan ne bayan da aka dawo daga hutu, kuma Mauro Icardi ya farke mata kwallo.

Kungiyoyin biyu sun kara ne a daya daga cikin wasanni 10 da aka fafata a gasar cin kofin Serie A wasannin mako na 17.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka fafata:

Palermo 5 - 0 Cagliari Udinese 0 - 1 Roma Chievo 0 - 0 Torino Empoli 0 - 0 Verona Genoa 2 - 2 Atalanta Milan 1 - 2 Sassuolo Parma 1 - 0 Fiorentina Cesena 1 - 4 Napoli