Sakho ba zai buga gasar kofin Afirka ba

Diafra Sakho
Image caption Senegal tana rukuni tare da Ghana da Afirka ta Kudu da kuma Algeria

Dan kwallon West Ham, Diafra Sakho, ba zai buga wa Senegal gasar cin kofin nahiyar Afirka ba, sakamakon ciwon baya da yake fama da shi.

Kocin Senegal ne Alain Giresse ya sanar da cewar Sakho ba ya cikin tawagar 'yan wasan kasar da za su wakilce ta a gasar.

Tun a ranar Talata aka sa ran dan kwallon mai shekaru 25, zai halarci Dakar domin auna girman ciwon nasa, amma bai samu zuwa ba.

Senegal ta maye gurbinsa da Pape Moussa Konete, mai shekaru 21, wanda yake taka leda a kulob din Sion da ke Switzerland.