LA Galaxy ta tabbatar da za ta dauki Gerrard

Steven Gerrard Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gerrard zai koma Amurka da taka leda a watan Yuni

Kociyan kulob din Los Angeles Galaxy na Amurka ya tabbatar da cewar Steven Gerrard zai koma taka leda da su a watan Yuni.

Bruce Arena ya shaida wa jaridar LA Times cewa kulob din zai bayar da sanarwa ta musamman a ranar Laraba.

Shi kuwa shugaban kulob din Chris Klein, ya bayyana komawar da Gerrard zai yi gare su da cewa zai karfafa musu gwiwa matuka.

Gerrard ya ce dalilin da yasa ya zabi komawa Galaxy saboda nasarorin da suke samu a harkar kwallon kafa ya ga ya da ce da shi ma ya bayar da tasa gudunmawar.