Hukumar kwallon kafar Asia za ta zabi Blatter

Ali Blatter Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Za a kalubalanci Blatter a zaben shugaban kujerar FIFA

Hukumar kwallon kafar Asia za ta marawa Sepp Blatter baya a takarar zaben shugaban FIFA, maimakon yarima Ali da ya sanar da zai tsaya takarar.

Yarima Ali na Jordan ya zamo na biyu da zai kalubalanci shugabancin kujerar FIFA, bayan da Jerome Champagne ya fara nuna aniyarsa.

Sakataren hukumar kwallon kafar Asia, Dato Alex, ya shaida wa BBC cewar mambobin hukumar sun amince za su zabi Blatter tun a taron FIFA na bara.

Sai dai sakataren ya kara da cewar ba zai hana mai kada kuri'a ya zabi abinda yake so ba, domin zabe ne na kashin kai domin tabbatar da dimokaradiyya.