Toure ne gwarzon dan kwallon Afirka karo na 4

Yaya Toure
Image caption karo na hudu a jere Yaya Toure yana lashe kyautar

Dan kwallon kafar Ivory Coast, Yaya Toure, ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afirka da ya fi yin fice A Afirka karo na hudu a jere.

Dan wasan ya lashe kyautar ne sakamakon gudunmawar da ya bai wa Manchester City wajen lashe kofin Premier da League Cup a bara.

Haka kuma ya taimakawa kasar sa samun tikitin buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a gudanar a Equatorial Guinea daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairu.

Toure ya lashe kyautar ne bayan da ya doke abokan takara da suka hada da dan kwallon Gabon Pierre-Emerick Aubameyang da golan Nigeria Vincent Enyeama.

An gudanar da bikin ne a birnin Legas, wanda ya taba daukar bakuncin bikin a shekarar 2008 da kuma 2013.

Ga jeren sauran kyautukan da aka lashe:

Dan kwallon da ya fi yin fice mai taka leda a Afirka

Firmin Mubele Ndombe (DR Congo and AS Vita)

Macen da ta fi yin fice a iya kwallo a Afirka

Asisat Oshoala (Nigeria and River Angels)

Matashiyar yar wasa da ta fi taka rawar gani

Asisat Oshoala (Nigeria and River Angels)

Matashin dan kwallo da yake tashe

Yacine Brahimi (Algeria and Porto)

Kociyan da ya fi haskakawa

Kheireddine Madoui (ES Setif)

Tawagar kwallon kafar Afirka da ba kamarta Maza

Algeria

Tawagar kwallon kafar Afirka da ba kamarta Mata

Nigeria

Kulob din da ya fi yin fice a Afirka

ES Setif (Algeria)

Alkalin da ya fi kwarewa

Papa Bakary Gassama (Gambia)