Defoe zai yi atisaye a Tottenham

Jermain Defoe Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Defoe tsohon dan kwallon Ingila da Tottenham

Tsohon dan kwallon Tottenham, Jermain Defoe, zai yi atisaye a kungiyar domin ya kasance kan ganiyarsa a lokacin da aka kammala gasar Amurka.

Defoe, mai shekaru 32, ya bar kulob din Tottenham ne a watan Fabrairun bara, inda ya koma taka leda a kulob din Toronto na Amurka.

Dan kwallon wanda yake yin jinya, ya zura kwallaye 11 a wasanni 16 da ya buga wa Toronto.

Tsohon dan kwallon Ingilan wanda ya buga wa kasar wasanni 363 ya kuma zura kwallaye 142, ana rade-radin zai koma murza leda a Ingila.