Sergio Aguero ya dawo atisaye da City

Sergio Aguero Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sergio Aguerro ya zura kwallaye 14 a gasar Premier

Dan kwallon Manchester City, Sergio Aguero, ya koma atisaye da kulob din, bayan jinyar da ya tafi a watan Disamba.

Aguero, mai shekaru 26, ya halarci atisaye da kulob din a safiyar Alhamis tare da Edin Dzeko wanda shi ma ya yi jinya tun daga watan jiya.

Sergio ya zura kwallaye 19 a cikin wasanni 17 da ya buga wa City, kafin ya tafi jinyar raunin da ya ji a karawar da suka yi da Everton ranar 6 ga watan Disamba.

Manchester City za ta kara da Everton a gasar Premier wasan mako na 21 ranar Asabar, kafin ta karbi bakuncin Arsenal a Ettihad.