Mathieu Debuchy zai yi jinya

Mathieu Debuchy Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya sha fama da yin jinya

Mai tsaron bayan kulob din Arsenal, Mathieu Debuchy, ya ji rauni a kafadarsa a lokacin da suka kara da Stoke City a gasar Premier a Emirates.

Dan wasan Faransa, mai shekaru 29, ya fado ne da kafada lokacin da ya yi karo da dan wasan Stoke Marko Arnautovic, kuma sai Hector Bellerin ya canje shi a karawar.

Debuchy, wanda ya koma Arsenal daga Newcastle a watan Yunin bara, ya yi fama da jinyar watanni uku sakamakon raunin da ya ji a kafarsa.

Kuma lokacin da yake yin jinya Calum Chambers ko kuma Bellerin ne suka dunga maye gurbinsa.