Arsenal ta doke Stoke City da ci 3-0

Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Arsenal ta koma matsayi na biyar a teburin Premier

Arsenal ta samu maki uku akan Stoke City bayan da ta doke ta da ci 3-0 a gasar Premier wasan mako na 21 da suka kara a Emirates ranar Lahadi.

Laurent Koscielny ne ya fara zura kwallon farko a raga da kai daga bugun da Sanchez ya yi wo.

Sanchez ne ya kara ta biyu bayan da suka yi bani in baka tsakaninsa da Tomas Rosicky kafin a ta fi hutu, sannan ya kuma kara ta uku daga bugun tazara.

Da wannan nasarar da Arsenal ta samu ya sa ta koma mataki na biyar a teburin Premier da maki 36, yayin da Sunderland ke matsayi na 16 da maki 20.