Ba zan bar Barcelona ba - Messi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Messi ya ce ya gaji da mutanen da ke tsegumi a kansa.

Dan wasan gaba na Barcelona, Lionel Messi, ya dage cewa ba zai bar kulob din ba duk da rade radin da ake yi cewa zai bar kungiyar.

Messi ya karyata rahotannin da ke cewa ya bukaci kociyan kulob din, Luis Enrique, ya sauka daga mukaminsa.

Rahotanni dai na cewa dan wasan, mai shekaru 27, yana son barin kulob din sakamakon rashin jituwa tsakaninsa da Enrique.

Messi ya ce, "Bani da niyyar zuwa kowane kulob; ba zan koma Chelsea ko Manchester City ba. "

Ya bayyana haka ne bayan Barcelona ya doke Atletico Madrid 3-1.

Messi ya kara da cewa,"Na gaji da tsegumin da ake yi a kaina. Ban bukaci a sauke kowanne mutum daga mukamisa ba."