Van gaal bai da-na-sanin ajiye Falcao ba

Hakkin mallakar hoto z
Image caption Van gaal da Falcao

Manajan Manchester United, Louis van Gaal, ya ce bai yi da-na-sanin kin zabar dan wasansa, Radamel Falcao, ba domin taka wa kulob din leda a wasan da Southampton ya doke su da ci 1-0 ranar Lahadi.

Van Gaal ya ce ba ya da-na-sanin kin daukar Falcao duk da cewar yana daukar tsabar kudi har fam dubu 265 a kowane mako.

Ya kara da cewa ya fi bukatar mai-tsaron gida, saboda haka babu wata rawa da dan wasan gaba mai mataki na biyu kamar Falcao zai taka.

Dan wasan na gaba -- mai shekaru 28 -- bai samu damar shiga ko da jerin 'yan wasan wucin-gadi ba, a wasan da kulob din ya buga a Old Trafford.

Yanzu dai Southampton yana gaba da Manchester United da maki biyu, bayan fadowar kulob din daga mataki na uku zuwa na hudu a tebirin Premier.