Aston Villa zai sayi Carles Gil kan £3.2m.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana sa rai Gil zai buga wasan da Villa zai yi da Liverpool

Kulob din Aston Villa na shirin sayen dan wasan Valencia, Carles Gil, kan kudi £3.2m.

Kociyan Villa, Paul Lambert ya dade yana son sayen dan kasar na Spaniya mai buga wasa a rukunin 'yan kasa da shekaru 21.

Gil ya zura kwallo daya a wasanni takwas da ya buga a gasar La Liga.

Idan dai cinikin ya fada, ana sa ran dan wasan zai buga wasan da Aston Villa zai fafata da Liverpool ranar Asabar.

Villa dai ya yi ta fama wajen cin kwallaye a gasar Premier, inda ya zura kwallaye 11 a wasanni 21 da ya yi.