Ban san makomata a Barcelona ba - Messi

Image caption Messi ya ce ba shi da tabbas kan abin da zai faru game da shi

Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya ce bai san makomarsa a kulob din ba duk da yake ya ce yana son ci gaba da zama a kulob din.

A cewarsa, "Ban san inda zan kasance ba a shekara mai zuwa."

Kyaftin din na Argentina ya yi watsi da zarge-zargen da ake yi cewa yana yunkurin barin kulob din, yana mai cewa "karya ce" kawai.

Sai dai da yake bayani a wajen ba da kyautar Ballon d'Or a Zurich ranar Litinin dan wasan -- mai shekaru 27-- ya ce "babu wanda ya san gobe."

Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo ne ya lashe gasar, lamarin da ya sa ya zama gwarzon dan kwallon kafa na duniya sau biyu a jere.

Da aka tambayi Messi cewa ko yana so ya gama rayuwarsa ta kwallon kafa a Barcelona ko kuma kulob din Argentina, Newell's Old Boys da ke garinsu Rosario, sai ya ce "Ba ni da tabbacin abin da zai faru, ko akwai yiwuwar komawa ta Newell's."