Shugaban Eq Guinea ya sayi tikitin wasa 40,000

Teodoro Obiang Nguema Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a fara gasar cin kofin Afirka ne ranar 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun 2015

Shugaban Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema, ya saye tikiti 40,000 domin bai wa yan kasar su kalli gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Equatorial Guinea ce ta maye gurbin Morocco wajen karbar bakuncin gasar a watan Disambar bara, kuma ana fargabar 'yan kasar ba za su halarci wasannin ba.

Manyan biranen kasar ne za su karbi bakuncin gasar da suka hada da Malabo da bata da Ebebiyin da kuma Mongomo.

Nguema ya ce ya sayi tikitan ne saboda 'yan kallon kwallon kafar kasar su cika filayen wasanni domin cin moriyar karbar bakuncin gasar da suka yi.

Morocco ce tun farko aka shirya za ta karbi bakuncin gasar bana, amma daga baya ta bukaci da hukumar kwallon kafar Afirka ta daga gasar daga ranar 17 ga watan Janairu nan, dalilin da ya sa aka maye gurbinta.