Di Maria ya amince da salon van Gaal a United

Angel di Maria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan ya koma United ne kan kudi sama da fam miliyan 59

Dan kwallon Manchester United, Angel Di Maria, ya ce yana goyon bayan sabon salon taka leda da koci Louis van Gaal yake koya musu.

Lokacin da yake jawabin nasa a gidan talabijin na Manchester United ya kara da cewar 'yan wasan suna fahimtar sabon salon da kocin ya kirkira.

Di Maria ya ce wasu jama'a na cewa ba ma taka leda kamar yadda ya kamata, kuma wannan ba salon wasan United ba ne, amma ai sabon tsari muke gwadawa.

Dan wasan na Argentina wanda ya yi jinya tun daga watan Nuwamba, ya buga karawar da Southampton ta doke su da ci daya mai ban haushi a Old Trafford ranar Lahadi.