Messi ba zai bar Barcelona ba — Enrique

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sai a shekarar 2019 ne kwantiragin Messi zai kare da Barcelona

Kociyan Barcelona, Luis Enrique, ya ce Lionel Messi ba zai bar kulob din ba, duk da rade-radin da ake cewar dan wasan bai san makomarsa ba.

Kwanakin baya ne Messi, mai shekaru 27, ya musanta maganganun da ake cewar zai bar Barcelona nan gaba.

Sai dai kuma kyaftin din na Argentina ya ce babu wanda ya san mai gobe za ta haifar a lokacin bikin kyautar gwarzon dan kwallon kafar da ya fi yin fi ce a duniya da aka yi a Zurich.

Kwantiragin Messi zai kare da Barcelona a shekarar 2019, kulob din da ya lashe kofunan zakarun Turai uku da na La Liga Shida, tun lokacin da ya fara buga masa kwallo a 2004.

Haka kuma ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya sau hudu, amma wannan karon Cristiano Ronaldo ne ya lashe kyautar.