Watakila Falcao zai bar Man United

Image caption Falcao ya yi fama da ciwon gwiwa tun da ya zo Old Trafford

Wakilin Radamel Falcao ya ce watakila dan wasan na Manchester United ba zai ci gaba da zama a Old Trafford ba har kakar wasa ta badi.

Dan wasan, dan kasar Colombian, wanda ke daukar £265,000 a kowanne mako, ya zura kwallaye uku a wasanni 13 da ya buga tun lokacin da aka sayo shi daga Monaco a kan £6m a watan Satumba.

Wakilin dan wasan, Jorge Mendes, ya ce "shi [Falcao] zai fara taka leda a daya daga cikin kulob mafi inganci a duniya a kakar wasa ta badi ko da kuwa kulob din Manchester United ko a'a".

Falcao dai ya yi fama da ciwon gwiwa tun zuwansa Old Trafford.