Babu isassun wuraren kwana a Eq Guinea

Claude Le Roy Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a fara gasar cin kofin Afirka ranar 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairu

Kungiyoyin da za su fafata a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a fara a Equatorial Guinea na fuskantar karancin masauki a kasar.

Kociyan Congo, Claude Le Roy, ya ce biyar daga cikin tawagar jami'ansa ba su samu wurin kwana ba.

Kociyan ya kara da cewar sauran 'yan wasan da suka samu masauki babu ruwa a bandaki, sannan kuma an bar wayar wutar lantarki tsirarar.

Kociyan Burkina Faso, Paul Put, shi ma ya yi korafin karancin abubuwan more rayuwa, inda ya ce ya kamata a dage gasar zuwa watan Yuni mai zuwa.

Equatorial Guinea ce ta maye gurbin Morocco daf da za a fara gasar a watan Nuwamba, sakamakon janyewar da ta yi saboda tsoron kamuwa da cutar Ebola.