Rukunin D

Hakkin mallakar hoto

Rukuni na hudu: Ivory Coast da Guinea da Mali da kuma Kamaru

Ivory Coast

 • Ta halarci gasar sau: 20
 • Kwazon da ta fi yi: Lashe kofin a shekarar (1992)
 • Kociyanta: Herve Renard (France)
 • Fitattun 'yan kwallonta: Yaya Toure da Wilfried Bony da kuma Gervinho
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 28.

Ivory Coast ta yi rashin nasara a wasan karshe a shekarar 2006 da kuma 2012. Rashin nasarar da ta yi a shekaru uku baya ta yi ne a hannun Zambia, wadda a lokacin Renard ke horar da kasar. Wannan gasar Didier Drogba ba zai buga wasannin ba domin ya yi ritaya daga buga wa kasar tamaula, amma kasar ce ta fi yawan zura kwallaye a raga a wasannin neman cancanta a inda ta ci kwallaye 13--kuma za ta samu karfin gwiwa ta wajen Bony dan wasan da ya kasance daya daga cikin 'yan kwallon kafar Afirka da ya fi karbar albashi mafi tsoka bayan da ya koma Manchester City kan kudi fam miliyan 28.

Mali

 • Ta halarci gasar sau: 8
 • Kwazon da ta fi yi: Zama ta biyu a shekarar (1972)
 • Kociyanta: Henri Kasperczak (Poland) Fitatcen dan kwallonta: Seydou Keita
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 50.

Mali tana kafa tarihi mai ban sha'awa a duk lokacin data samun tikitin buga gasar. A gasa takwas baya da ta halarci gasar sau shida tana kai wa wasan daf da na karshe, ta kuma kai mataki na uku a gasa biyu baya da aka fafata. Kasar ta bada mamakai a lokacin da suka kara da Angola a shekarar 2010 a wasan farko na bude gasar, bayn da aka ci su 4-0 kuma saura mintuna 11 sai da suka farke kwallayensu aka tashi wasan 4-4.

Kamaru

 • Ta halarci gasar sau: 16
 • Kwazon da ta fi yi: Ta lashe kofin a (1984, 1988, 2000, 2002)
 • Kociyanta: Volker Finke (Germany)
 • Fitattun 'yan kwallonta: Stephane Mbia da kuma Vincent Aboubakar
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 42.

Kamaru ba ta samu halartar gasar 2012 da kuma 2013, kuma ta kasa tabuka rawar gani a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil. Duk da haka Kamaru ta manta da dukkan abubuwan da suka faru a baya har da ritayar da Samuel Eto'o ya yi suka kuma samu tikin gasar bana ba tare da an doke su ba. Aboubakar da Clintton N'Jie ne suka ciwa Kamaru kwallaye shiga daga ciki tara da ta ci.

Guinea

 • Ta halarci gasar sau: 10
 • Kwazon da ta fi yi: Ta zama ta biyu a shekarar (1976)
 • Kociyanta: Michel Dussuyer (France) Fitatcen dan kwallonta: Ibrahima Traore
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 39.

Kasar Guinea ta samu tikitin buga gasar bana duk da bullar annobar cutar Ebola da ta barke a kasar, kuma dalilin da ya sa ta kasa buga wasanninta a gida, ta kuma zabi komawa wasa kasar Morocco. Wannan ne karo na uku da kociyan Dussuyer zai zagoranci kasar a gasar cin kofin Afirka, a inda ya fara jagorantar tawagar kwallon kafar kasar tun a gasar da Tunisia ta karbi bakunci shekaru 11 da suka wuce.