Za a bude gasar kofin Afirka ranar Asabar

Hakkin mallakar hoto
Image caption Za a fara gasar cin kofin Afirka ranar Asabar

Kasar Equatorial Guinea za ta yi bukin bude gasar cin kofin Afirka karo na 30 da karfe 1600 agogon GMT, inda za ta kara da Congo a Bata.

Wasa na biyu shi ma a filin Bata za'a buga tsakanin Burkina Faso da Jamhuriyar Congo da karfe 19 agogon GMT.

Equatorial Guinea ta maye gurbin Morocco ne, bayan da kasar ta bukaci hukumar kwallon kafar Afirka ta dage gasar sakamakon tsoron kamuwa da cutar Ebola.

Tuni kuma kasar ta shirya karbar bakuncin wasannin a filaye hudu da suka hada da Malabo da Bata da Mongomo da kuma Ebebiyin.

Kasashe 16 ne za su kara a gasar da ake sa ran kammata ranar 8 ga watan Fabrairun bana, kuma mai rike da kofin Nigeria bata samu tikitin shiga gasar ba.