Zambia da Jamhuriyar Congo sun buga 1-1

Zambia DRCongo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zambia za ta kara da Tunisia a wasan gaba ranar Alhamis

Wasan farko a rukuni na biyu tsakanin Zambia da Jamhuriyar Congo sun tashi kunnen doki a gasar cin kofin nahiyar Afirka da suka buga ranar Lahadi.

Singuluma ne ya fara ci wa Zambia kwallo a minti biyu da fara wasa, kafin daga baya Yannick Bolasie ya farke kwallon a minti na 66.

Jamhuriyar Congo ta kai hare-hare da dama musamman ta hannun 'yan wasanta Bolasie da kuma Dieumerci Mbokani.

Ranar Alhamis ne za'a ci gaba da wasa na biyu a rukunin tsakanin Tunisia da Zambia da kuma karawa tsakanin Jamhuriyar Congo da Cape Verde.