Mourinho ya yaba wa 'yan wasan Chelsea

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Chelsea za ta ziyaci Liverpool ranar Talata a gasar League Cup

Kociyan kulob din Chelsea Jose Mourinho ya yaba wa 'yan wasansa ta yadda suka doke Swansea City da ci 5-0 a gasar Premier ranar Asabar.

Chelsea ta zura kwallayenta biyar ne ta hannun Oscar da Diego Costa da kowannensu ya zura biyu a raga sannan Andre Schurrle ya ci ta biyar an kusa tashi daga wasan.

Maurinho ya ce wasan ya yi kyau matuka kuma 'yan wasa sun murza leda kamar yadda ya umarce su su yi.

Sai dai kocin ya bukaci 'yan wasan su lashe kofin bana, domin idan ba haka ba babu wanda zai tuna da irin wannan kokarin da suka yi.

Chelsea tana mataki na daya a teburin Premier da maki 52, bayan buga wasanni 22, za kuma ta ziyarci Liverpool ranar Talata a gasar League Cup.