Sinkala ya ji rauni ya hakura da kofin Afirka

Nathan Sinkala Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Zambia za ta kara da Tunisia ranar Alhamis a Ebebiyin

Dan kwallon tawagar Zambia Nathan Sinkala ba zai ci gaba da buga wasannin gasar kofin Afirka ba, sakamakon raunin da ya ji ranar Lahadi.

Dan wasan mai shekaru 24 ya ji rauni ne a gwiwarsa a lokacin da suka tashi wasa kunnen doki da Jamhuriyar Congo a wasannin rukuni na biyu.

Likitan tawagar Zambia, Joseph Kabungo, ne ya sanar wa da hukumar kwallon kafar kasar cewar dan wasan zai yi jinyar makonni hudu kafin ya warke.

Jinyar da Sinkala zai yi, za ta kawo wa Zambiya koma baya a gasar, ganin yana daya daga cikin fitattun 'yan wasan tawagar.

Zambiya za ta kara da Tunisia a wasa na biyu a rukuni na biyu ranar Alhamis.