Wasanmu da Chelsea zai zama manuniya - Pellegrini

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Pellegrini ya ce dole ne su doke Chelsea idan ba haka ba akwai matsala.

Kociyan Manchester City, Manuel Pellegrini, ya ce karawar da za su yi da Chelsea za ta zama kazaran-gwajin-dafi a yunkurinsu na kare kambunsu a gasar Premier.

Kulob din City dai ya fado daga saman tebirin Premier, yayin da Chelsea ya hau bayan Arsenal ta bi su har gida ta doke su da ci 2-0, lamarin da ya sa suka yi asarar maki biyar.

Chelsea zai karbi bakuncin City ranar 31 ga watan Janairu, kuma Pellegrini na sane cewa dole ne su doke Chelsea idan ba haka ba za su cire ransu daga kare kanbunsu.

Ya ce,"Wasan da za mu yi a Stamford Bridge yana da matukar muhimmanci. Dole ne mu cike gibin da muke da shi na rashin maki biyu da muka yi."

Pellegrini ya kara da cewa, "Yana da matukar muhimmanci mu yi nasara a wasan da za mu da Chelsea. Ina fata za mu wartsake, mu taka leda kamar yadda muke yi."