Ivory Coast da Guinea sun tashi wasa 1-1

Gervinho
Image caption Ivory Coast da Guinea suna da maki daya kowannensu

Ivory Coast da Guinea sun tashi kunnen doki a gasar cin kofin nahiyar Afirka wasan rukuni na hudu da suka kara a Bata ranar Talata.

Guinea ce ta fara zura kwallo saura mintuna tara a ta fi hutun rabin lokaci ta hannun dan wasanta Mohamed Yattara, kafin Seydou Doumbia ya farke saura minti takwas a tashi daga wasan.

Ivory Coast ta karasa wasanta da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka kori fitatcen dan kwallonta Gervinho a minti na 58 da aka yi ana fafatawa.

Za a ci gaba da karawa a rukuni na hudun ne tsakanin Mali da Ivory Coast, sai kuma wasa tsakanin Guinea da Kamaru ranar Asabar.