Mali da Kamaru sun tashi kunnen doki

Mali Cameroon Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kamaru za ta kara da Guinea a wasa na biyu ranar Asabar

Tawagar kwallon kafar Mali ta tashi wasa kunnen doki da Kamaru a gasar cin kofin nahiyar Afirka wasa na biyu na cikin rukuni na hudu da suka kara ranar Talata.

Mali ce ta fara zura kwallo ta hannun Samuel Yatabare a minti na 71, daga baya Kamaru ta farke kwallonta saura mintuna shida a tashi wasan ta hannun Oyongo Bitolo.

Da wannan nasara ya sa Ivory Coast da Guinea da Mali da kuma Kamaru dukkansu suna da maki daya a tsakaninsu.

Za kuma su buga wasanni na biyu a cikin rukunin tsakanin Mali da Ivory Coast, sai karawa tsakanin Guinea da Kamaru ranar Asabar.