Suarez zai koma kan ganiyarsa — Enrique

Barcelona Atletico Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Barcelona tana matsayi na biyu a teburin La Liga

Kociyan Barcelona, Luis Enrique ya ce sabon dan wasansa Luis Suarez zai koma kan ganiyarsa ta zura kwallaye a raga.

Suarez, dan wasan Uruguay ya ci wa Barcelona kwallaye uku a wasanni 12 da ya buga mata tun lokacin da ta dauko shi daga Liverpool kan kudi fam miliyan 75.

Daya daga cikin kwallayen da ya zura ita ce wadda ya ci Atletico Madrid, za su kara da ita a gasar Copa del Rey wasan daf da na kusa da karshe ranar Laraba.

Enrique ya ce "aikin Suarez ne cin kwallaye kuma dalilin da ya sa muka dauko shi ke nan, na san yana daf da dawo wa kan ganiyarsa ta zazzaga kwallaye a raga".

Atletico na fatan lashe kofin karo na biyu a cikin shekaru uku, bayan da ta dauki kofin a shekarar 2013.