A yi gasar maza da mata a lokaci daya - Ginola

David Ginola Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ginola zai kalubalanci Blatter a takarar kujerar FIFA

Mai shirin takarar kujerar shugabancin hukumar kwallon kafar duniya, David Ginola, ya ce kamata ya yi a dunga buga gasar cin kofin duniya ta maza da ta mata a lokaci daya.

Ginola, mai shekaru 47, ya kara da cewar idan har za a dunga buga gasar a tare, hakan zai bunkasa gasar kwallon kafa da kuma daga darajar wasannin mata a harkar tamaula.

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, tana shirya gasar cin kofin duniya ta maza da kuma ta mata a kasashe daban a kuma shekaru da suka banbanta.

Ginola ya bayar da misalin cewar a gasar cin kofin da aka kammala a Brazil da sai a fara karawa a wasannin mata a filayen da aka yi amfani da su a Brazil din.

Haka kuma ya ce zai dawo da martabar hukumar FIFA a idon duniya, ganin yadda hukumar ta bari batun cin hanci da rashawa ya dabaibaye ta.