Mun sauya Mirallas ne saboda ya ji rauni - Martinez

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu dai na ganin an cire Mirallas ne saboda ya kasa cin bugun fenareti

Kociyan Everton, Roberto Martinez ya ce an sauya Kevin Mirallas a wasan da suka yi kunnen-doki da West Brom ne sabosa ya ji rauni ba domin ya kasa cin bugun fenareti ba.

Dan wasan baya, Leighton Baines ne ya fi yi wa kulob din bugun fenareti, amma a wasan da suka yi da West Brom ya bar Mirallas ya buga, kuma bai yi wata-wata ba wajen buga kwallo waje.

Kociyan ya ce duk da haka babu wani babu.

Sai dai mataimakin kociyan Ingila Gary Neville, ya ce an cire Mirallas ne saboda ya kasa cin bugun na fenareti.