Arsenal ya kammala sayen Bielik

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An gwada lafiyar dan wasa

Kulob din Arsenal ya sayi matashin dan wasan nan na Legia Warsaw, Krystian Bielik kan kudi £2.4m.

Bielik, mai shekaru17, wanda aka kammala gwajin lafiyarsa a Arsenal din a makon jiya, ya koma Legia daga Lech Poznan a watan Yulin da ya wuce.

Sau shida ya taka leda a kulob din a duk wasannin da suka fafata a kakar wasa ta bana.

Bielik zai iya buga wasa a tsakiya da baya.