'Masu ci wa Arsenal kwallo a bana sun fi na 2006'

Arsenal Strikers Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana matsayi na biyar a teburin Premier

Dan kwallon Ingila, Theo Walcott, ya ce 'yan wasan Arsenal da suke buga wasan gaba a bana sun fi yin fice fiye dana lokacin su Thiery Henry.

Walcott, wanda ya koma Arsenal a shekarar 2006, ya kuma taka leda tare da 'yan wasan da suka gagara a shekarar 2003-04 da suka hada da Thierry Henry da kuma Dennis Bergkamp.

Sai dai kuma dan wasan ya ce hadakar Alexis Sanchez da Olivier Giroud da Danny Welbeck da kuma Alex Oxlade-Chamberlain sun fi yin kwazo da kwarewa fiye da na lokacin Henry.

Arsenal wacce take mataki na biyar a teburin Premier da maki 39, za ta karbi bakuncin Aston Villa ranar Lahadi 1 ga watan Fabrairu.