Eto'o ba zai bar Everton ba — Martinez

Samuel Eto'o Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sampdoria ce ta bayar da sanarwar daf take da ta dauko Eto'o

Kociyan Everton, Roberto Martinez, ya ce babu wata maganar cewar Samuel Eto'o na daf da komawa kulob din Sampdoria na Italiya.

Sampdoria ya sanar a farkon makonnan, cewar yana shirin kammala dauko Eto'o mai shekaru 33 da haihuwa domin buga masa wasa kafin karshen makon.

Sai dai Martinez ya ce " Ba haka kawai za su saki dan wasan ya koma taka leda a wani kulob din ba, dole sai sun yi binciken fa'idar barin dan kwallon idan ya bar su".

Eto'o ya koma Everton ne kan yarjejeniyar kwantiragin shekaru biyu a watan Agusta, kuma ya zura kwallaye hudu daga cikin wasanni 20 da ya buga.