Liverpool zai iya kai wa wasan karshe - Rodgers

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Brendan Rodgers ya yabawa Sterling

Kociyan Liverpool Brendan Rodgers ya ce kulob din zai iya kai wa wasan karshe na Gasar cin Kofin Capital One duk da cewa sun tashi da ci 1-1 da Chelsea a wasan farko na dab da na karshe a Anfield.

Eden Hazard ne dai ya ci wa Chelsea kwallonta yayin da Raheem Sterling ya fanshe a bugun fenareti.

Rodgers ya ce,"Ina ganin rawar da muka taka ita ce za ta auna yadda muke taka leda. Hakan ya bani kwarin gwiwar cewa za mu je Stamford Bridge mu yi wasan da za mu yi nasara."

Rodgers ya yabawa Sterling saboda kwazon da ya nuna "na musamman".