Bayanai 5 kan kungiyoyin da suka fi arziki

Man United Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester United tana matsayi na hudu a teburin Premier

Kulob din Real Madrid ya ci gaba da rike kambun wanda ya fi arziki a duniya shekaru 10 a jere dai-dai da yawan lashe kofin zakarun nahiyar Turai da ya yi wanda mujallar Deloitte ta fitar.

Har yanzu manyan gasar wasannin kasashe biyar ne suka mamaye yawan kungiyoyin dake kan gaba da suka hada da gasar Premier Ingila da Bundisligar Jamus da Seria A ta Italiya da La Ligar Spaniya da kuma gasar Faransa ta Ligue 1.

Kungiyoyi 14 ne daga cikin gasar Premier suke cikin ajin 30 din farko da suka fi arziki, bayan da ake shirin sabunta kwantiragin nuna wasanni nan ba da jimawa ba, kuma hakan ya sa ake hasashen kungiyoyin gasar Premier za su kara karuwa a cikin jerin wadanda suka fi arziki a duniya.

Bari mu duba yadda aka fitar da rahoton binciken.

Har yanzu Real Madrid ce kan gaba a duniya

Bayan da Real Madrid ta lashe gasar cin kofin zakarun Turai karo na 10 a watan Mayun bara, da kuma lashe kofin zakarun nahiyoyi a watan Disamba da ya wuce, hakan ya sa ta ci gaba da rike kambunta na kungiyar kwallon kafa da ta fi arziki a duniya.

Madrid din ta samu kudin shiga da ya kai sama da dala miliyan 630 a karshen watan yunin 2014, ciki har da karin kaso 10 cikin dari kan nuna wasanninta da kuma tallace-tallace.

Haka kuma kulob din na Spaniya ya samu daukar dan kwallon Norway mai shekaru 17 da haihuwa Martin Odegaard.

Manchester United za ta iya zama matsayi na biyu a jere

Rashin samun kyakkyawan sakamako a wasanni kamar yadda suka saba a baya, ya kawo wa Manchester United tsaiko, amma hakan bai hana ta samun kudin shiga ta hanyar tallace-tallace ba, musamman yarjejeniyar da suka kulla da kamfanin General Motor wadda ta fi kowacce tsada a duniya, inda zai sa riga ta kamfanin da kuma kayan wasanni na Adidas kan kudi fam miliyan 750 na tsawon shekaru 10.

Rashin samun gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da kulob din ya kasa a bara zai iya kawo wa kulob koma baya a jerin rahoton a badi, amma idan kulob din ya samu gurbin shiga gasar a bana hadi da kudin nuna wasanninta da kuma kudaden tallace-tallace da take samu, hakika Manchester United za ta iya darewa matsayi na daya a kulob din da ya fi arziki a shekarar 2017.

Kungiyoyin Burtaniya ne suka mamaye rahoton

Kungiyoyi daga Burtaniya da dama na cikin 30 din farko a rahoton -- hakan ya nuna martabar gasar Premier ta yarjejeniyar nuna wasanni da kungiyoyin ke samu da ta kai fam biliyan uku daga shekarar 2013-16.

Kuma takwas daga kungiyoyin Premier suna cikin ashirin din farko, matsayin da suka rike shekaru shida da suka wuce--inda kungiyoyin Burtaniya 14 suka cikin talatin din farko.

Manyan kungiyoyin Ingila dake kan sawun gaba sun hada da Man United da Manchester City da Chelsea da Arsenal da kuma Liverpool wadan da dukkansu suke cikin goman farko.

Ba lashe kofi bane mafi mahimmanci

Yadda Manchester United ta koma mataki na biyu, ya bayyana a fili cewar ba lashe kofi bane zai sa ka taka rawa a jerin kungiyoyin da suka fi yin arziki a duniya.

Haka kuma Liverpool ta koma mataki na tara daga matsayinta a baya na 12, wacce bata dauki kofi ba a baran, haka ita ma Tottenham da ta kare a mataki na shida a gasar Premier ta kara gusawa zuwa sama a rahoton.

A kasar Spaniya, Atletico wadda ta lashe kofin La Liga a bara ta koma mataki na 15 daga matasyinta na 20 a baya, koda yake rashin taka rawar ganin Barcelona a bara ya kawo mata koma baya, a inda ta koma mataki na hudu, kuma karon farko da ta koma matsayin tun daga shekarar 2007-08 da ta rinka zama a mataki na biyu a rahoton.

Sauran binciken da rahoton ya fitar

Kulob din Galatasaray na Turkiya shi ne wanda yake cikin 'yan 20 din farko da baya daga cikin manyan gasar kungiyoyin Turai biyar.

Kulob din Napoli na Italiya na cikin na farko da ya shiga jerin 'yan ashirin din farko bayan da ya samu karin kudin shiga da ya kai kaso 50 cikin dari a bara, wanda suka kare a matsayi na uku a gasar Serie A ta Italiya.