An ci tarar Aston Villa fam 60,000

Villa Leicester Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester ce ta doke Aston Villa da ci daya mai ban hausi a wasan

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ci tarar Aston Villa fam 60,000, saboda rashin da'a da 'yan wasanta suka nuna a wasan da suka yi da Leicester City.

'Yan wasan kulob din ne suka dinga tayar da yamutsi a waje da kuma a cikin fili, har sai da da aka kori dan wasan Leicester Matty James da Ciaran Clark na Villa daga fili.

Dukkansu kungiyoyin biyu sun amsa tuhumar da hukumar ta yi musu tun a farkon makon nan har ma ta ci tarar Leicester fam 20,000.

Wannan shi ne karo na uku da aka ci tarar Villa a inda ta fara biyan fam 20,000 da kuma fam 30,000, saboda kasa tsawatarwa 'yan wasanta, lokacin da suka kara da Tottenham da kuma Manchester United.