Real Madrid zai sayi Martin Odegaard

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An dade ana rade radin cewa Odegaard zai koma wani kulob din Turai

Real Madrid ya sanya hannu kan yarjejeniyar sayen Martin Odegaard daga Stromsgodset.

Kulob din zai gabatar wa manema labarai dan wasan, mai shekaru 16 a ranar Alhamis.

Real bai bayyana adadin kudin da zai sayi dan wasan ba sai dai kafafen watsa labaran Spaniya sun rawaito cewa za a saye shi ne kan euro 3m.

Odegaard ya fara taka leda a Norway yana da shekaru 15 a watan Agusta, kuma tun a lokacin ake rade radin zai koma wani daga cikin kulob din Turai.