Kun san kulob din da ya fi kudi a duniya kuwa?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lissafin bai hada da bashin da ake bin kulob-kulob din ba

An bayyana Real Madrid a matsayin kulob din da ya fi kowanne kulob kudi a duniya.

Wannan shi ne karo na goma a jere da kulob din ke zama kulob din da ya fi tsabar kudi a duk fadin duniya.

Deloitte ne ke zabar kulob din da ya fi kudin.

Manchester United ya zakuda daga mataki na hudu zuwa na biyu a cikin wadanda suka fi kudi bisa harajin da ya karba a shekarar 2013-14.

Bayern Munich, da Barcelona da Paris Saint-Germain ne suka zo na uku da na hudu da na biyar a jere.

Manchester City, da Chelsea, da Arsenal da Liverpool su ne na shida da na bakwai da na takwas da kuma na tara a jerin wadanda suka fi kudi.

Tottenham ne na13, yayin da aka samu sababbin kulob-kulob da suka shiga jerin, kamar su Newcastle United da Everton, inda suka zama na 19 da 20.

Kiyasi ya nuna cewa harajin da kulob-kulob guda ashirin da suka fi kudi a duniya suka karba ya kai €6.2bn.

Lissafin dai bai hada da bashin da ake bin wadannan kulob-kulob ba.