Mourinho ya ji kunyar cire su daga FA

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana matsayi na data a teburin Premier

Kociyan Chelsea, Jose Mourinho, ya ce ya ji kunya da takaici kan yadda aka yi waje da su daga gasar kofin kalubale da Bradford City mai buga League One ta yi.

Chelsea ce ta fara zura kwallaye biyu a Stamford Bridge kafin Bradford City ta farke ta kuma doke ta da ci 4-2.

Haka ita ma Manchester City an yi waje da ita a gasar, bayan da Middlesbrough ta doke ta da ci 2-0 a Ettihad.

Maurinho ya ce "Abin kunya ne karamar kungiya ta fitar da babba a gasa, saboda haka da shi da 'yan wasansa sun ji kunya matuka".

Haka ma Manchester United ta tashi wasa babu ci da Cambridge United, a inda Blackburn Rovers ta yi waje da Swansea City daga gasar ta FA.